Tsohon dan wasan Madrid din zai maye gurbin tsohon abokin wasansa Santiago Solari
Tsohon kocin Real Madrid ya shirya tsaf don dawowa filin wasa na Bernabeu a matsayin koci a karo na biyu.


Zidane zai maye gurbin Santiago Solari ne wanda ya jagoranci kulob din na kusan tsawon wata biyar.
Tsohon dan wasan tsakiyar Madrid din me shekara 46, ya bar horar da kulob din bayan ya jagorance su lashe gasar Zakarun Turai ta Champions Leage karo na uku a jere.


Yanzu haka Madrid suna mataki na uku a teburin La Liga, maki 12 a kasan Barcelona wadda ke saman teburi da maki 63.
Ana sa ran kungiyar za ta raba gari da kocinta Solari biyo bayan nasarar 4-1 da ta samu a kan Real Valladolid ranar Lahadi, wadda ta biyo bayan kashin da ta sha a hannun Ajax ta kasar Netherlands a gasar Zakarun Turai.