Yan Najeriya na shirin kada kuri'a don zaben shugabannin da za su ja ragamar kasar a matakin shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki.
Misalin karfe 8:00 na safiyar Asabar agogon Najeriya ake sa ran bude rumfunan babban zaben wanda aka dage tsawon mako daya saboda matsaloli da suka shafi raba kayan zabe a sassan kasar.
'Yan takara sama da 70 ne ke neman darewa kujerar shugaban kasa a zaben, amma Shugaba Muhammadu Buhari na APC mai shekara 76, da abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na PDP, mai shekara 72 ne suka fi jan hankali a zaben.
Shugaba Buhari ya ce ya aza tubalin ci gaban kasar, amma Atiku Abubakar ya ce an samu koma-baya kan sha'anin tsaro da tattalin arziki da makamantasu a gwamnatin Buhari.
Ana ganin zaben 2019, shi ne mafi girma a tarihin Afrika inda ake sa ran mutum miliyan 84 za su kada kuri'a a zaben na Najeriya kasa mafi girma a nahiyar Afirka.
Hukumar zaben kasar ta tabbatar wa 'yan Najeriya cewa ta shirya wa zaben bayan kalubalen da ta fuskanta na raba kayan zabe wanda ya tilasta ma ta dage zaben da ka ranar 16 ga Fabrairu zawu 23 ga fabrairu na 2019.

0 Comments