Tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk wanda ya saci akwatin zabe ya yi a bakin ransa, 'yan kasar suke ta cece-kuce a kan wannan kalamai na sa.
A wannan dalili ne ya sa BBC ta tuntubi wani lauya
a Najeriya watau Dakta Aminu Gamawa, a kan ko me
doka ta ce a kan wanda ya saci akwati.
Dakta Aminu dai ya bayyana cewa dokar kasar ta
hana sace akwatin zabe kuma duk wanda aka samu
da laifin yin hakan, za a iya yanke masa hukuncin
zaman gidan yari na kusan shekaru biyu.
Ya bayyana cewa idan aka kama barawon akwatin
zabe, jami'an tsaro su kamashi su bincike shi
sa'annan a gurfanar dashi gaban kotu.
Ku latsa hoton da ke sama don sauraron hirar
Barista Aminu Gamawa.
Lauyan ya kuma ce bai kamata a ce idan an kama
barawon akwatin ba an dauki doka a hannu, ya ce
kotu ce kadai ke da hurumin hukunta shi.
An dade ana fama da batun satar akwatin zabe a
Najeriya a lokacin zabe inda ake samun 'yan
barandan siyasa suna irin wannan aika-aika.
Tuni dai wasu manya a jam`iyyar APC suka ce
shugaban kasar gargadi ne kawai yake yi.
inda suka ce jama'a da dama sun jahilci kalaman na
shugaban kasa.
Babbar jam`iyyar hamayyar kasar dai, wato PDP ta yi
zargin cewa shugaban kasar na so ne ya yi amfani da
jami`an tsaro wajen dakile `yan adawa.