kwana biyu ya rage a fara babban zabe a Nigeria inda muka tattauna da wani matashi a garin Kano dake Nigeria inda ya bawa Matasa shawara a kan zaman lafiya a zaben mai zuwa a ranan 16 ga watan febrairu na shakarar 2019 inda ya bawa matasa shawara kamar haka:

"Sai dai wani hanzari ba guduba: Rai daya ne a gangar jikin mu, karmu ba dashi ga wanda baisan munayi ba, ma'ana kada mu sadukar da rayuwar mu akan wani Dan siyasa, Zabe ba yaki bane, quri'arka/ki ce yancin ka/ki, hayaniya ko rashin da'a basa kawo zaman lafiya, duk abin da hakuri baiba dashi ba rashinsa ba zai ba dashi ba,muje zabe lafiya, muyi zabe lafiya, mubar filin zabe lafiya, Allah yayi mana zabi Na Alkhairi, amin "

 Sadeeq L Muhd ya shaidawa shafin Smart Arewa ta wayar hannu bayan mun tattuna da shi gama da zabe mai zuwa na ranar 16 ga wanna watan.