Shugaban Nigeria kuma dan takarar Shugaban kasa a karo na biyu
Muhammadu Buhari na jam`iyyar (APC) da tsohon mataimakin shugaban Najeriya
wato Alhaji Atiku Abubakar wazirin Adamawa dan takarar jam`iyyar adawa ta
PDP za su sanya hannu akan amincewar sakamakon zaben takarar shugaban
kasa na 2019 da za a yi ranar 16 ga Watan Fabirairu.
A makon nan ne tsohon shugaban Amurka Bill Clinton zai gana da
Shugaba Buhari da kuma Atiku Abubakar don samun damar gudanar da zabe
cikin zaman lafiya, kamar yadda kakakin tsohon shugaban Angel Ureña ya sanar.
Kwamitin zaman lafiya na kasa wanda tsohon shugaban Najeriya
Abdulsalam Abubakar ke jagoranta suka sanar da hakan.

0 Comments