Dan wasan tsakiya na Argentina Jabier Mascherano ya yi ritaya daga bugawa kasar ta Argentina kwallo bayan da aka fitar da su daga gasar cin kofin duniya a ranar Asabar din data gabata. Dan kwallon mai shekara 34 ya bugawa kasar wasa sau 145, ciki har da wanda suka sha kashi a hannun Faransa da ci 4-3 a zagayen ‘yan kungiyoyi 16 na gasar a ranar Asabar. Mascherano ya buga dukkan wasannin da Argentina ta yi a gasar cin kofin duniya a Rasha kuma ita ce ta hudu da ya halatta a jere a tarihi. Ya shaidawa manema labarai cewa “Ni dai a wuri na, komai ya zo karshe domin daga yanzu ni ma magoyin bayan Argentina ne kawai.” Dan kwallon wanda ya lashe lambar zinare ta Olympic sau biyu, ya fara bugawa kasar Argentina  wasa ne a 2003, kuma ya fara kwallo ne a kungiyar Riber Plate dake kasar Argentina. Ya buga kwallo a kungiyoyin West Ham da Liverpool da kuma Barcelona sai dai a yanzu yana buga wasa ne a kasar China tare da kungiyar Hebei China Fortune.