Tsohon gwanman Kano kuma Sanata a jam'iyyar APC yace zai iya kayar da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Injiniya Rab'iu Musa Kwankwaso ya ce shi yanzu ba shi da wata jam'iyya amma PDP ce ta fi kowacce dama da karfin kayar da shugaban, idan har ta ci gaba da bin tafarkin demokuradiyya."PDP na bukatar tsayar da mutumin da ya fito daga jihohin Kano, Katsina ko Kaduna takarar shugaban kasa idan har tana son yin nasara domin su ne jihohin da suka fi ko'ina yawan kuri'u," in ji shi. Sannan ya ce shi ne ya fi kowa "cancantar yi wa jam'iyyar takara".
Tsohon mataimakin shugaban kasa Abubakar, wanda dan jihar Adamawa ne, da tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido, da na Kaduna Ahmed Makarfi, da na Kano Malam Ibrahim Shekarau na cikin wadanda suka bayyana aniyarsu ta neman takara a PDP.
Sai dai a kwanakin baya Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai kuma na hannun damar Shugaba Buhari, ya ce kwankwaso ba zai kayar da Buhari zabe a Kano ba a badi.
Kalaman na Kwankwaso na zuwa ne 'yan kwanaki bayan ya kauracewa babban taron jam'iyyar APC na kasa, yana mai cewa an nuna ba a yi da shi.
Sanatan na cikin shugabannin bangaren tsaffin 'yan PDP wanda ya kunshi Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, da na Wakilai Yakubu Dogara, da suka yi zargin ana muzguna musu a APC kuma gwamnatin Buhari ta mai da su saniyar-ware.
Zargin da jam'iyyar da gwamnatin suka musanta, kuma an fara tattaunawa domin duba korafe-korafen nasu.

0 Comments