Yunkurin Barcelona na kafa tarihin kammala wasanni a gasar La liga ba tare an doke ta ba ya gamu da cikas.
Kungiyar Levante ce dai ta doke Barcelona da ci 5-4 a wasan da suka buga ranar Lahadi.Tun da farko dai Levante ta lallasa ta ne da ci 5-1 inda Emmanuel Boateng ya zura kwallaye uku yayin da Enis Bardhi ya zura kwallaye biyu.
Barcelona dai ta buga wasanni 44 a gasar La Liga ba tare da an doke ta ba inda ta shafe tarihin da Real Sociedad ta kafa na buga wasanni 38 ba tare da an doke ta ba a kakar wasa ta 1979/80.
Masu sharhi na ganin kocin Barcelona zai yi takaicin hutun da ya bai wa Lionel Messi.
Suna ganin da dan kwallon ya buga da zai yi wuya a doke Barcelona.
Messi ne ya fi kowa cin kwallon a gasar ta La Liga ta bana

0 Comments