Ma'aikatar harkokin cikin gida ta haramta duk wata zanga-zanga bayan fasa ofisoshin jam'iyya mai mulki tare da ɓarnata kayayyaki, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a jamhuriyar Nijar.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce “Duk wani nau'in zanga-zanga ta haramta a yanzu. Hukumomi za su tabbatar kowa ya yi biyayya ga doka da kuma hukunta waÉ—anda suka karya ta.”

Ma'aikatar ta jaddada cewa hukumomi ba za su lamunci É“arnata dukiyar Æ™asa da wasu marasa kishi ke yi ba kuma dole a É—auki mataki. 

Ta kuma buƙaci jami'an tsaro su tabbatar sun kare dukiyar jama'a da ta gwamnati.