An haramtawa masu shaguna a kasuwar waya ta Farm Centre da ke jihar Kano lika hotuna ko sauraron wakokin shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido a shagunansu.
Kamar yadda mai sanarwar ya bayyana, shugaban kasuwar, Hassan Abubakar Bawasa shine ya bayar da umurnin, yana mai gargadin cewa duk wanda aka kama ya karya dokar zai dandana kudarsa.
Ya kara da cewar an sanya takunkumin ne sakamakon batancin da Davido ya yi wa addinin Musilan ce, addinin gaskiya.
"Dukkan wanda ya san ya lika hoton Davido da ya gaggauta cire shi ya banka masa wuta, sakamakon batancin da ya yi wa addinin gaskiya, addinin Allah, addinin mutanen kasuwar waya na Farm Centre.
"Bayan haka, sanya odiyo ko bidiyo na Davido a teburinka ko a shagonka ya zama haramun a kasuwar waya ta Farm Centre. Idan aka kama ka, za a dauki kwakkwaran mataki na ladabtarwa ta yadda za ka dandana kudarka. Sanarwa daga Hassan Bawasa."
wani Gidan Jarida mai suna Legit.ng ta tuntubi Mallam Bashir Ibrahim wanda ya kasance dila ne a kasuwar wayan inda ya tabbatar da dokar.
Mallam Bashir Ibrahim ya ce: "Eh tabbas da gaske ne an saka wannan doka daga hukumar kasuwar." Da aka tambaye shi game da tasirin da wannan doka yi mallam Bashir ya ce lallai ya yi tasiri domin sun daina jin wakar a kasuwar. Ya ce: "Ai yayi tasirima tunda mun dai najii."
Asali: Legit.ng https://hausa.legit.ng/news/1546402-bidiyon-batanci-haramta-lika-hoton-davido-ko-saka-wakarsa-a-

0 Comments