Zinedine Zidane zai ja ragamar Real Madrid wasa na 100 a La Liga a karawar da za ta karbi bakuncin Eibar a gasar mako na 31 ranar Asabar.
A wasan farko da suka a La Ligar bana, Eibar ce ta yi nasara da ci 3-0 ranar 24 ga watan Nuwambar 2018, kuma Gonzalo Escalante da Sergi Enrich da kuma Kike suka ci mata kwallayen.
Wannan ne karo na biyu da Zidane ya karbi aikin horas da Real, kuma wasa na hudu da zai yi, tun bayan da ya maye gurbin Santiago Solari.
Kocin ya ya yi nasara a kan Celta Vigo da Huesca a gasar La Liga a karo na biyu da ya koma Bernabeu, inda ya yi rashin nasara a hannun Valencia da ci 2-1 a wasan mako na 30 ranar Laraba.
Cikin jan ragamar Madrid da Zidane ya yi, ya ci wasa 70 da cin kwallo 269 da kungiyar ta yi, sannan ya jagoranci lashe kofin na La Liga a 2016/17 kuma na 33 da ta dauka a tarihi.
Bayan da ya horas da karamar kungiyar Real, Zidane ya karbi aikin kocin babbar Madrid ranar 4 ga watan Janairun 2016, kwana biyar tsakani ya doke Deportivo de La Coruna 5-0.
Real Madrid tana ta uku a kan teburin La Liga da maki 57, Atletico Madrid ce ta biyu da maki 62, sai Barcelona mai maki 70 a mataki na daya.
Sauran wasannin da za a buga na mako 31 ranar Asabar a La Liga:
- Girona da Espanyol
- Rayo Vallecano da Valencia C.F
- Barcelona da Atletico de Madrid
Ranar Lahadi kuwa 7 ga watan Afirilu
- Deportivo AlavesCD Leganes
- Getafe da Athletic de Bilbao
- Real Valladolid da Sevilla FC

0 Comments