Najeriya tana bukatar shuwagabanni irin su Sarkin Kano Sunusi(II).

Kamar yadda kuka saba ji sunana Umar Kabir Sorondinki dalibi wato dan makaranta.

A nazarin danayi wato hasashe na, yabani tabbacin muna bukatar shuwagabanni a kasar Najeriya irinsu Sunusi lamido Sunusi wato sarkin jahar Kano dake cikin kasar Najeriya a yankin Afurica ta yamma.

Dalilina shine anan; Sarki Sunusi (II) irinsu kadan ne a Najeriya domin masu iya magana sunce "shi sanin maza jari ne" Amma arziki babu me maka sedai a baka jari, domin Allah gwanin kyauta shikade kesan kirari saboda shi zaimaka yau idan ka gode, Gobe yayi maka kari!

A kullin yaumun a Najeriya muna da rauni a zukatanmu na son kanmu da yan uwanmu batare da tunawa cewa Najeriya bata mutum daya bace tareda iyalansa ba, da yan uwansa ba... Kamar kullin Sunusi(II) mutum ne me son Al ummah kuma baya kyamar dan uwansa talaka kasan cewa shi sarki ne amma, anmasa shedar hakan tun yana gwamnan bankin najeriya har kawo iyanzu.

Sannan ya kasance mai kishin kasarsa da son cigabanta a kullu yaumin, kullin tunaninsa baya wuce mai zai kawo cigaban rayuwar yan kasarsa wajan tallafa musu da shawarwari ya kuma basu abinda zasuci da taimako iri-iri.

Kunga kuwa Najeriya tana bukatar me irin wannan halayyar saboda se mun sowa kanmu abinda muka sowa yan uwanmu sannan za'a samu chigaba a rayuwarmu ta yau da kullum

Najeriya kasa ce wadda tazamo me tarin arziki na man fetur, Sannan munada kasa me albarka wajan yin Noma a bangaren Arewa dake sashin Najeriya

Wannan dalilin ya isa ayi duba me kyau.
Domin cigaban al'ummah a kasa gabadaya.

Source: (Mai rubutu: Umar Kabir Soron dinki,  Email: uksdinki@gmail.com)



      Dont Forget to Comment and Share the Post!!