Mai kula da harkokin tamaular Gareth Bale, ya caccaki magoya bayan Real Madrid da rashin dattako, bayan da suka yi wa dan wasan ihu a karawa da Barcelona a ranar Asabar.
Magoya bayan Madrid sun yi ta yi wa Bale ihu a lokacin da Marco Asensio zai sauya shi a wasan hamayya da Barcelona ta ci 1-0 a Santiago Bernabeu.
Jonathan Barnett ya ce ya kamata magoya bayan Real su tuna kwallayen da ya ci wa kungiyar zuwa shekaru da dama, amma sun ji kunya da halin da suke nuna masa.
''Gareth ya cancanci girmamawa, amma yadda magoya bayan Real Madrid ke yi masa abin takaici ne.''
- Bale ya lashe kofin Zakarun Turai hudu, ya kuma ci kwallo 101 a wasa 218 tun komawarsa Real Madrid daga Tottenham kan fam miliyan 85 a 2013.
Sai dai kuma Bale ya kasa maye gurbin Cristiano Ronaldo dan kwallon tawagar Portugal wanda ya koma taka-leda a Juventus a farkon kakar bana.
Barnett ya ce duk masu yin rubutu kan Bale ba su san shi ba, bai kuma yi hirar cewar zai bar Madrid ba, zai kuma ci gaba da zama a Real domin abin da yake kauna kenan.

0 Comments