A yanzu haka abin da 'yan kasar suka zura ido su gani shi ne irin gumuruzun da za a yi a zaben na gwamna a ranar Asabar.
Akwai jihohi kalilan da tuni aka yi hasashen 'yan takarar da za su lashe zaben jihohin sakamakon karancin karfin jam'iyyun adawa.
A wasu jihohin kuma, kamar mace ce mai ciki, ba a san abin da za ta haifa ba, saboda girman adawa tsakanin 'yan takara a jihohin inda da wuya a iya hasashen wanda zai iya lashe zaben gwamna a jihohin.
Jihohin da ake ganin zaben gwamna zai fi zafi sun hada da Kano da Sokoto da Kaduna da Gombe da Lagos da Akwa Ibom da Imo.

Sharhi, Mustapha Kaita
Kamar yadda ake yi wa kallon siyasar Kano sai dan Kano kuma 'Kano ta dabo tumbin Giwa, ko da me ka zo an fika,' hakan ya sa ake ganin zaben gwamna a 2019 a Kano zai fi zafi fiye da sauran jihohin.
Za a fafata ne tsakanin gwamna mai ci da ke neman tazarce Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da kuma dan takarar Kwankwasiyya Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP.
Ana ganin zaben gwamna Kano, fafatawa ce tsakanin tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon mataimakinsa gwamna Ganduje wadanda suka yi shekara takwas a gwamnati.
A Kaduna kuwa ana ganin zaben gwamna zai ja hankali musamman tsakanin 'yan takarar manyan jam'iyyun siyasa wato APC da kuma PDP.
Gwamnan Kaduna Malam El-Rufai dan takarar APC zai fafata ne da babban mai hamayya da shi Isah Ashiru Kudan na jam'iyyar PDP, kuma a yanzu haka masu sharhi na cewa tui siyasar jihar ta dauki bangaranci na addini da kabilanci.
Gombe na daga cikin jihohin da ake ganin za su ja hankali a zaben gwamna.

Jam'iyyar APC mai adawa za ta yi kokarin kwace mulki ne daga hannun jam'iyyar PDP da ke mulka a jihar.
Za a fafata ne tsakanin Usman Bayero Nafada na jam'iyyar PDP da kuma dan takarar jam'iyyar APC Inuwa Yahaya, wacce ake gani tamkar tsakanin gwamna mai barin gado ne Hassan Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Danjuma Goje.
A Sokoto kuwa, Gwamna Tambuwal ne ke neman tazarce a wa'adi na biyu inda zai yi takara tare da tsohon mataimakinsa Ahmed Aliyu wanda APC ta tsayar dan takararta kuma wanda tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko ke marawa baya.

0 Comments