Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya shaida wa BBC cewa ba su taba raba kudi ba domin su sayi kuri'un jama'a.


Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf ya shaida wa BBc cewa ba su taba raba kudi ba domin su sayi kuri'un jama'a.

Ya bayyana wannan ne a wata hira da aka yi da shi kai tsaye a shirin yamma na ranar Talata da BBC ke gudanarwa.

Abba ya bayyana cewa a shirye suke da su karbi zaben da za a sake yi a ranar 23 ga watan Maris hannu biyu domin su sun yi "imani da kaddara."