Hajiya Aishatu Jibril Dukku, 'yar majalisa wakilai mai wakiltar mazabar Dukku da Nafada a majalisar wakilan Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda aka bar mata a baya a harkokin siyasa.
Ta bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ta yi da BBC, kuma ta ce ana nuna wa mata bambanci tun a mazabu saboda ana ganin mace ba za ta iya wakiltar jama'arta ba.
Kuma ta ce idan aka bai wa mata dama sau da yawa su na fin maza kokari. 
A cewarta, ko a majalisar wakilai idan aka samu gurbin da mace ta sauka sai a bai wa namiji dama maimakon a bai wa wata macen.
Shi ya sa ma yawan matan da ke majalisar dokokin Najeriya ya ragu.
Ta ce hakan kuma ba ya rasa nasaba da tunanin mutanen arewa da ke ganin mace ba za ta iya wakilci ba da kuma rashin samun tallafi daga bangarori da dama.
Ta ce shi ya sa ko a bangaren ilimi mace ta zama koma baya.
Ta ce sau da yawa, akwai mukaman da mata ya kamata su rike kamar mukamin shugaban mata amma sai a bai wa namiji don kawai ana ganin macen ba ta cancanci ta rike mukaman ba.
"A nan Senegal, dokarsu ta yi tanadin duk mukami idan namiji ne a kai to mace ce za ta zama mataimakiyarsa. Me zai hana ba za sa irin wannan dokar ba a Najeriya?", inji Aishatu Dukku.
Ta kuma nuna damuwarta kan yadda ba a bai wa mata dama ba a zabukan fitar da gwani na 2018 ba.
A cewarta, mata da yawa sun siya fom din 'yan takara a dukka jam'iyyun amma ba a basu takarar ba.
Ta ce wannan kuma ba ya rasa alaka da irin shugabancin da ake da shi a jam'iyyun.
'Idan aka samu shugabanci mai adalci za a ga sakamako mai kyau, idan kuma akasin haka ne za a ga sakamako marar kyau."
Tarihi dai ya nuna cewa mata a Najeriya sun taka muhimmiyar rawa a fagen siyasa, duk da kalubale da dimbin matsalolin da su ke fuskanta a kasar da har yanzu ke da sauran burbushin tsattauran ra'ayi.
A shekarun da suka gabata, an mayar da mata koma baya a fannin ci gaba a Najeriya duk da cewa sama da kashi hamsin cikin dari na mutanen Najeriya mata ne.