Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona ta lallasa kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid da ci 3-0 a Wasan kusa da na karshe na cin gasar kofin kasar Spanish wato Copa Del Rey, Wanda hakan ya ba wa Kungiyar Barcelona damar zuwa matakin karshen na cin Gasar kofin Copa del Rey.
Kungiyar Kwallon Kafa ta Madrid dai yanxu haka anyi waje da ita daga cin Gasar Kofin, Kafin Wasan dai Kungiyar Madrid ta zo filin was an Barcelona wato Camp Nou inda Kungiyoyi Biyun suka tashi da ci daya a kowacce Kungiya.
A Zuwa da Barcelona tayi Filin wasa na Madrid wato Santiago a yau shine ya bata damar lallasa Kungiyar da Madrid, da farko dai an fara wasa, inda har aka juya hutun rabin wasa babu ci ko daya daga kowacce kungiya.

0 Comments