Sojoji dauke da manyan makamai sun rufe
ofishin yanki da Hedkwatar kanfanin
Jaridar Daily Trust a Biranen Maiduguri da
Abuja, kan labarin kwace garin Baga da
Jaridar ta ce mayakan Boko Haram sun yi.
Mataimakin babban Editan Jaridar Daily
Trust, Mallam Mahmoud Jega, ya shaidawa
Sashen Hausa cewa, sojojin sun isa wurin
suna neman wani dan jaridar kamfanin mai
suna Hamza Idriss, amma basu sameshi ba,
sai suka umarci duk ma'aikatan dake bakin
aiki su bar wurin ba tare da bata lokaci ba, Su
ka garkame kamfanin bayan sun kashe baki
daya na"urorin kamfanin.
Mahmud ya ce, can ma a ofishin kamfanin
dake Arewa maso gabashin Najeriya sojojin
sun je suna neman Hamza Idriss, amma da
basu sameshi ba suka cafke wasu ‘yan jaridun
kamfanin guda biyu.
Mataimakin babban editan yakara da cewa,
hakan baya rasa nasaba da labarin da Jaridar
ta buga cewa, mayakan Boko Haram sun
fatattaki sojojin daga garin Baga, sannan ta
kara buga labarin cewa sojojin na tattaruwa
domin sake kwato garin na baga.
Tuni dai kungiyar ‘yan jaridun Najeriya ta yi
Allah wadai da wannan mataki na sojojin tana
mai bayyana cewa barazana ne ga
dimokradiyya.
Amma mai magana da fadar shugaban
Najeriya Mallam Garba Shehu, ya fitar da
wata sanarwa wadda ta umarci sojojin dasu
janye daga kamfanin jaridar ta Daily trust.

0 Comments