Me Kungiyar Kwallon Ta Chelsea Roman Abramovic
Bayan da rade-radi suka yi karfi akan cewa me kungiyar Chelsea, Roman Abramovic na shirin sayar da kungiyar akan kudi mafi tsada da aka taba sayar da wata kungiyar kwallo Kwallon Kafa tun bayan Manchester United. Kungiyar Kwallon Kafa Ta Chealsea ta fito ta musanta wadannan rahotanni.

Me kungiyar dai yana tsaka da rashin jituwa da gwamnatin kasar Ingila bayan da suka hanashi bizar shiga kasar, shi kuma ya nufi kasar Isra'ila ya yanki katin zama dan kasa, dalilin hakane wata majiya ta bayyana cewa Abramovic wanda attajirin gaske ne dan kasar Rasha ya saka Chelsea a kasuwa yana neman Yuro miliyan dubu 2.5.




Saidai wani rahoto da ya fito daga jaridar The Mirror ya bayyana cewa Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea tace me kungiyar yana nan kan  ra'ayinshi na rike Chelsea  bazai sayar da ita ba.