Fitaciyyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-fina hausa na Kannywood wato Hadiza Aliyu Gabon ta ja hankalin mabiya shafinta na zumunta da cewa su hankalta da masu bude shafuka na bogi da sunanta.
Jarumar ta wallafa wani shafi na bogi da aka bude da sunan ta wanda ke rokon jama'a da su tallafa da kudi domin tallafawa marasa karfi.
Ta nisantar da kanta daga shafin tare da yin kira ga jama'a da su kauracewa ire-iren shafukan bogi masu bukatar kudi daga masu bibiyan ta.wannan yana daya daga cikin abubuwa dake ci ma jaruman kannywood tuwo a karya yadda ake yawan bude shafukan bogi da sunan su, tare da neman kudi daga jama'a.

0 Comments