Andres Iniesta, wanda ya zura kwallon da ta bai wa Spain damar lashe gasar kofin duniya a 2010 ya yi ritaya daga buga wa spain wasa bayan da Russia ta doke spain a wasan cin kofin duniya na 2018.
Dan kwallon mai shekara 34 an sako shi ne bayan an dawo hutun rabin lokaci a wasan da Spain ta sha kashi a hannun Rasha da ci 4-3 a bugun fanareti a zagayen 'yan 16 ranar Lahadi.
Kwallon karshe da Iniesta ya buga ita ce fanaretin da ya ci a wasan wanda shi ne na 131 da ya buga wa kasar.
Iniesta, wanda ya fara bugawa kasar spain kwallo a 2006, ya kuma lashe gasar kasashen Turai a 2008 da 2012. A watan Mayu ne Iniesta ya kawo karshen shekara 22 da ya shafe a Barcelona inda ya koma kulob din Vissel Kobe na kasar Japan.
Ya lashe kofuna 32 a Barcelona, inda ya buga wa babbar tawagar kungiyar wasa 674 bayan da ya fara a karamar tawagar tun yana dan shekara 12.