Dan wasan Argentina Lionel Messi ya ce sun sha bakar wahala a wasan da suka buga da Najeriya jiya inda suka lallasa Najeriya da ci biyu da daya, wanda ya yi sanadiyar yin waje da Najeriya.

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kammala wasan, Messi wanda shi ne kwallo na farko a wasan ya ce mun sha “bakar wahala” gaskiya a wannan wasa.
“Wasan ba laifi, mun fi Najeriya taka leda kafin hutun rabin lokaci, mu zata haka za a ci gaba bayan rabin lokacin, amma kwatsam sai suka farke kwallo dayan ta hanyar bugun daga kai sai gola, wanda hakan ya dawo da hannun agogo baya. Shi ne sai muka shiga tsoro kuma hankalinmu ya tashi matuka.”
 Wasan dai an buga shi a kasa Rasha a ranar talata, inda Argentina ta buge Nigeria da ci 2-1